Connect with us

Featured

Wata Gobara Ta Tashi A Babbar Kasuwar Gamboru Da Ke Maiduguri Jihar Borno

Wata mummunar gobara ta sake tashi a kasuwar Gamboru da ke kusa da unguwar Kwastam a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Makamancin haka ta faru a ranakun 18 ga Maris, 2023 da 13 ga Nuwamba, 2023, inda gobara ta kone kasuwar da aka ce ita ce babbar kasuwar kayayyaki a Maiduguri.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno, Alhaji Usman Tar, ya ce gobarar ta tashi ne a Layin Yan Katako da kuma kewayen wajen kasuwar.

Kwamishina Usman Tar a cikin wata sanarwa ya ce lamarin wanda ya faru a ranar Laraba da misalin karfe 10 na dare, jami’an hukumar kashe gobara ne suka yi nasarar kashe su.

“Ba tare da bata lokaci ba hukumar kashe gobara ta jihar Borno ta aike da tawagar jami’an kashe gobara zuwa wurin da lamarin ya faru kuma an kashe gobarar yadda ya kamata.

“Ba a bayar da rahoton asarar rayuka ba. Tsaron kasuwar ba ya cikin hadari ko barna,” inji shi.

A cewarsa, hukumar kashe gobara da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar suna gudanar da aikin tantance afkuwar lamarin domin gano musabbabin faruwar hakan da matakan kaucewa afkuwar lamarin nan gaba.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta dauki dukkan matakan shawo kan bala’o’in da ke faruwa a jihar.

Ya shawarci jama’a da su kiyaye doka da oda tare da tabbatar da cewa ba a keta haddin kasuwar ba.

“A madadin gwamnatin jihar Borno, muna jajantawa duk wadanda wannan lamari ya shafa.

“Muna kuma gode wa masu ba da taimakon gaggawa saboda saurin da suka yi wanda ya hana gobarar yaduwa a sauran sassan kasuwar,” in ji shi.

(NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet