Featured
Gwamnan Kogi Ya Tabbatar Da Kama Bata Garin Da Suka Kai Hari Wasu Yakuna A Jihar
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo, ya sanar da kama wadanda ake zargi da hannu a rikicin da ya barke a garin Bagana na karamar hukumar Omala a makon jiya.
A makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka mamaye al’ummar yankin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 25 tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira.
Gwamnan, yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Larabar nan jim kadan bayan kammala Sallar Eid Fitr a filin Sallah na Okene, ya ce an kama wadanda suka aikata wannan aika-aika, da kuma wadanda suka dauki nauyinsu, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano yawan wadanda aka kama.
Ya yi kakkausar suka ga masu sukar gwamnati, yana mai bayyana su a matsayin “masu munafunci da kuma rashin samu dama a ruwa da tsaki a harkar mulki.”
“Mayar da martani ga munafukai wadanda ba su da hannu a harkar mulki ba ya cikin aikin da mutanen jihar Kogi da kuma shugaban kasa suka ba ni.
“Ba yau aka fara rikicin Bagana a karamar hukumar Omala ba. Ya kasance sama da shekaru 45 da suka gabata, daidai 1978. Muna yin iya ƙoƙarinmu don ganin an dawo da zaman lafiya a yankin.
“A yayin da nake magana da ku a yau, an kama wadanda ake zargi da daukar nauyin shirin kuma ana ci gaba da bincike.
“Suna ba mu bayanai masu amfani da za su kai ga kama wasu da ake zargi. Da zarar mun kammala wannan bincike, za a sanar da jama’a rahoton,” inji gwamnan.
Sai dai gwamnan bai bayyana adadin wadanda ake zargin da aka kama ba.
Shaidun gani da ido sun shaidawa PUNCH Online a Lokoja a ranar Juma’ar da ta gabata cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis inda ‘yan bindigar suka kai wani hari da aka bayyana a matsayin harin ramuwar gayya tare da mamaye al’ummomi biyu na yankin.
An ce ‘yan bindigar na fafatawa ne da mayakan Agatu a jihar Benue.
