Connect with us

Featured

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Wani Uba A Wata Shari’ar Rashin Kula Da Iyali

Babbar kotun jihar Akwa Ibom da ke zamanta a Uyo ta bayar da umarnin tsare wani Mista Itoro Monday Uko a karamar hukumar Ikot Ekpene da ke jihar bisa laifin cin zarafin kotu.

An ce Itoro Uko ya yasar da matarsa ​​da Dansa daya tilo da ya haifa mai shekara biyu a kauyen domin ya zauna da budurwarsa a Garin Ikot Ekpene.

Alkalin kotun, Mai shari’a Ntong Ntong, ya ba da umarnin ne bayan sauraron lauyan wanda ya shigar da kara kuma mahaifiyar yaron, Barista Ekom Friday Inwang, biyo bayan rashin halartar wanda ake zargin da kuma Lauyansa.

Mai shigar da karar, wani malamin makaranta mai zaman kansa daga karamar hukumar Mkpat Enin ta shaida wa kotun cewa baya ga yin watsi da nauyin da ya rataya a wuyansa na Uba wajen biyan bukatun yaronsa, wanda ake kara ya kuma ki mayar da bashin Naira 200,000 da ta karba wa mijinta don gyara motarsa ​​tun watan Maris din 2022.

Ta ce sun yi aure ne a ranar 18 ga watan Janairun 2020, kuma auren ya albarkace ta da ‘ya ta fari, bayan da ta samu ciki na biyu a lokacin da mijinta ya fara dukanta, wanda hakan ya sa ta rasa cikin.

Ko da rana daya mijinta bai taba zuwa dubata ba. Ta kara da cewa ‘yan uwanta ne suka biya mata kudin magani.

Ta shaida wa kotun cewa sai da ta je kauyensu da ke Mkpat Enin don mahaifiyarta ta kula da ita har sai ta warke sosai, kuma a tsawon zamanta, mijinta bai kira waya ko ziyarartarta ba.

Bayan ta warke ne a ranar 4 ga watan Yulin 2022, mai shigar da karar ta ce ta je gidan dangin mijinta da ke Itak Ikot Udo, inda suke zaune, domin ta gano dalilin da ya sa mijin nata bai ziyarceta ba, amma abin ya ba ta mamaki, sai aka canza musu makullin gidansu. Ba za ta iya shiga gidan ba don ɗaukar kayanta ko na ɗanta.

Misis Itoro Uko ta ce bayan ta haifi danta na fari, mijin nata yana Kawo mata dama kuma kokarin da ake na ganin ya sauya ya ci tura.

Ta ce ta sake samun juna biyu a karo na uku, kuma halinsa ya ci gaba, lamarin da ya sa surikanta suka ba ta shawarar ta zauna da iyayenta a Mkpat Enin don gudun kada mijinta ya kashe ta.

Lauyan wanda ya shigar da karar ya bukaci Kotun da ta bayar da umarnin kama wanda ake kara tare da tsare shi saboda rashin bin umarnin da kotun ta bayar a ranar 6 ga watan Afrilun 2023.

Mai shari’a Ntong ya ba da wannan umarni kuma ya umurci “Kwamishanan ‘yan sanda na Jihar Akwa Ibom da Baturen ‘yan sanda shiyyar ta Ikot Ekpene, da jami’ansu da sunan Gwamnan Jihar Akwa Ibom da Sufeto Janar na ‘yan sanda da su sa aka kama su tare da tsare su, Mista Itoro Monday Uko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu” sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis, 25 ga Afrilu, 2024, domin sauraren karar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet