Connect with us

Featured

Wasu Yara Uku ‘Yan Gida Daya Da Wasu Biyu Sun Rasu A Cikin Mota

Rundunar ’Yan sanda ta tabbatar da mutuwar wasu kananan yara biyar sakamakon rashin iska saboda kulle kansu a cikin wata mota a garin Minna, babban birnin Jihar Neja.

Yaran sun hada da mata hudu da namiji daya, ’yan uwa uku da wasu biyu daga iyaye daban-daban ciki har da dan mai motar.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce, ofishinsu da ke Kpakungu ya samu rahoton cewa an tsinci gawar yara biyar ’yan shekara biyar zuwa 13 kulle a cikin wata mota kirar Honda Civic a unguwar Gurara Albishir da ke Minna.

Abiodun ya ce an gano nunfashin yaran ne ya shake ya dauke a cikin motar, bayan da iyayensu da makwabta suka kwashe awannin suna neman su.

Ya ce daga bisani aka sanar da ’yan sanda suka ziyarci wurin.

A cewarsa, rundunar ta gayyaci mai motar domin yi masa tambayoyi kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Wata majiya a unguwar da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, yaran sun yi kuskure ne suka kulle kansu a cikin motar wadda mai gidan ya yi watsi da ita sama da shekaru biyu.

Ya ce daga baya ne iyayen suka gano gawarwakinsu a cikin motar a ranar Lahadi da yamma bayan sun shafe sa’o’i suna neman su a unguwar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet