Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Na Bincikar Shugaban Gidan Talabijin Na ARTV

Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da cin hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta ƙaddamar da bincike dangane da zargin almundahana kan Shugaban Gidan Talabijin na jihar (ARTV), Alhaji Mustapha Adamu Indabawa.

Binciken na zuwa bayan ƙorafin da Ƙungiyar ’Yan Jaridu (NUJ) da Ƙungiyar Ma’aikatan Gidajen Rediyo da Talabijin (RATTAWU) suka gabatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Borno: Dakarun Civilian JTF 8 Sun Rasa Ransu Sakamakon Taka Wani Bam Da Mayaƙan ISWAP Suka Dasa

Ƙungiyoyin na zargin Alhaji Indabawa da almundahanar kuɗin da suka kai Naira miliyan ɗari da kuma saɓa ka’idar aiki.

Ana iya tuna wa cewa Alhaji Indabawa na ɗaya daga cikin shugabannin hukumomi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa a watannin baya bayan nan.

Bayanai sun ce masu binciken sun titsiye Alhaji Indabawa a ranar Juma’ar da ta gabata kan zargin sama da-faɗin fiye da Naira miliyan 60 da kuma zargin satar tsabar kuɗi har Naira miliyan uku na Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da ya yi ikirarin an sace a cikin motarsa.

Minista Ya Yi Murabus Saboda Matsalar Daukewar Wutar Lantarki A Saliyo

Duk laifukan da ake zargin Alhaji Indabawa sun ci karo da sashe na 26 na Kundin Dokokin hukumar PCACC kuma mafi ƙanƙantar hukuncin shi ne cin sarƙa ta shekara uku.

A yayin da Aminiya ta tuntubi Alhaji Indabawa dangane da taƙaddamar, ya ce ba shi da ta cewa tunda har lamarin yana gaban hukuma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet