Featured
Bincike: Shedikwatar Tsaro Ta Sanar Da Cewa Akwai Ganganci A Harin Tudun Biri
Binciken Rundunar Sojin Kasar nan kan harin “kuskure” da jirgin sojin sama ya kashe Kusan mutane 100 a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, ya nuna akwai ganganci a cikin harin.
Bayan daukar dogon lokaci tana bincike kan harin rundunar sojin ta ce, jami’an da suka yi wannan aika-aika za su fiskanci hukunci.
Ta ce ta samu wasu jami’an rundunar biyu da hannu dumu-dumu wurin faruwar lamarin, kuma tabbas za su fuskanci hujuncin kotun soji, domin binciken su ya tabbatar da cewa tun farko bai kamata a saki bama-baman da aka jefa ba.
Daraktan yada labarai na shedikwatar tsaro ta Kasar nan, Edward Buba, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja ranar Alhamis.
Tun da farko dai rundunar ta dauki alhakin harin, sai dai a wancan lokacin ta danganta lamarin da “kuskure.”
Da yake karin haske, Edward Buba, ya ce an mika rahoton binciken ga wadanda suka dace, amma ba zai iya bude komai a kan lamarin ba har sai an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotun soji.
