Featured
‘Yan Sanda Sun Kama Mutum Bakwai Da Laifin Fashi Da Makami, Da Masu Asiri
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ce ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata ayyukan asiri da kuma fashi da makami.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya fitar a ranar Asabar, inda ya kara da cewa, sun kuma kwato wata karamar bindiga mai baki guda biyu, babur guda uku da babu lambar rajista da kuma wasu miyagun kwayoyi.
Ikenga ya ce jami’an ‘yan sanda suna farautar wani Makuo Nwuso, wanda aka fi sani da “Baby,” da kuma wani mutum da har yanzu ba a samu sunansa ba.
Ya kara da cewa, ‘yan sandan da ke aiki da rundunar ‘yan sanda ta musamman da ke yaki da ‘yan kungiyar asiri a lokacin da suke sintiri a mahadar UNIZIK da ke Awka, sun kama dukkan maza biyar da ke cikin babur, ciki har da direban babur.
Ya ce, “A ranar 3/4/2024 da karfe 10 na dare, rundunar ‘yan sandan jihar ta kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da ‘yan fashi da makami su bakwai, sun kwato wata karamar bindiga mai baki guda biyu, babur guda daya mara lambar reg, da wasu miyagun kwayoyi.
“Wadanda ake zargin sun hada da Chukwuemka Ozoekwe mai shekaru 18, Chidozie Anagor mai shekaru 18, Chukwuemeka Oyeoka mai shekaru 18, Ebuka Okoye mai shekaru 17, Olisa Obi mai shekaru 19, Chidubem Nwakwu mai shekaru 20 da Nwankwo Kosisochukwu dukkansu maza. Yayin da ake neman Makuo Nwosu da aka fi sani da Baby da wani mutum daya wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba.
Ya kara da cewa mutanen da ke cikin motar sun bi diddigin su yayin da sauran suka tsere, kuma aka kama wadannan.
Ikenga ya kara da cewa mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da harkokin kudi da mulki kuma mai rikon mukamin kwamishinan ‘yan sanda DCP Fidelis Ogarabe ya bukaci jami’an da su dage wajen yaki da miyagun laifuka a jihar.
