Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Batun Yiwuwar Kafa Sansanin Sojin Amurka Da Faransa

 

Gwamnatin Tarayya ta musanta batun cewa tana duba yiwuwar bai wa ƙasashen Amurka da Faransa damar kafa sansanin soja a ƙasar nan.

Wata sanarwa da Minista Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya aike wa BBC ta ce wannan batu “ba shi da tushe” kuma “gwamnatin tarayya ƙarƙashin mulkin Bola Ahmad Tinubu ba ta yin wata tattaunawa da kowace ƙasa game da hakan”.

A ƙarshen makon da ya gabata ne wasu cibiyoyi da manyan mutane a arewacin Kasar nan suka rubuta wa gwamnatin wasiƙa suna gargaɗin kada a bai wa ƙasashen damar kafa sansanin soji a Najeriya, bayan korar su da aka yi daga wasu ƙasashen yankin Sahel.

“Muna neman jama’a su yi watsi da wannan ƙaryar,” a cewar sanarwar.

“Ba mu samu wata buƙata ko tattaunawa da wata ƙasa ba kan wannan batu game da kafa sansanin wata ƙasar waje a Najeriya. Da ma tuni Najeriya na ci gaba da amfana daga aikin haɗin gwiwa wajen daƙile matsalolin tsaro.”

Tuni dai ƙasashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka fatattaki sojojin Faransa da na Amurka daga ƙasashensu kuma suka gayyaci na Rasha.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet