Connect with us

Featured

Ana Zargin Wani Harin ‘Yan Bindiga Ya Hallaka Mutum 6 Tare Da Jikkata Wasu Da Dama

Al’ummar Ambe da ke Arak a karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna a daren ranar Lahadi sun fuskanci harin ‘yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar mutane shida tare da jikkata wasu takwas.

A cewar wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, harin ya faru ne ba tare da wani rikici tsakanin al’ummomin da ke makwabtaka da su ba, lamarin da ke nuni da cewa harin wasu ’yan ta’adda ne suka kai musu.

Yayin da gwamnatin jihar Kaduna ba ta ce uffan ba a hukumance kan lamarin, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jema’a da Sanga, Daniel Amos, ya fitar da wata sanarwa da kakkausar murya kan harin.

A cikin bayanin nasa, Amos ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da asarar rayuka da aa samu a wannan kazamin harin.

Ya kuma yi tir da harin a matsayin wani yunkuri na kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma, inda ya yi kira da a gaggauta kai dauki domin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin hukunta su.

Yawan Kai Hari Ya Tilastawa Mazauna Wasu Kauyuka 10 Barin Muhallansu A Kaduna

Amos ya bukaci mazauna karamar hukumar Sanga da su kwantar da hankulansu a duk lokacin da suke cikin mawuyacin hali, yana mai tabbatar musu da cewa ana kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.

Ya kuma jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’ummar yankin domin tabbatar da tsaro da jin dadin duk mazauna yankin.

A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce an kashe mutane biyar, sannan kuma an kama mutum daya da ake zargi.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma tabbatar wa da al’umma cewa za ta ci gaba da kama duk wadanda suka aikata wannan danyen aiki da kuma tabbatar da doka da oda a jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet