Featured
Wani Mutum 1 Ya Rasu, Yayinda Wasu 75 Suke Asibiti Bayan Cin Wani Gurbataccen Abinci
Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta fitar da sanarwar wani mutum da ya gamu da ajalinsa yayin da wasu 75 kuma aka kai su asibiti, bayan cin wani abinci da ake zargin gurbatacce ne a Riyadh babban birnin kasar.
Rahotanni daga kafafen sada zumunta na cewa mutanen sun ci wata waina ce daga wani babban Kanti da ke Riyadh.
Kawo yanzu dai ma’aikatar ta bayyana cewa, ‘yan kasar Saudiyya 69 ne abin ya shafa, sai kuma wasu baki guda shida wadanda ba ‘yan asalin kasar ba ne ke karbar magani sakamakon cin abincin da ake zargin akwai kwayoyin cuta Clostridium botulinum a ciki.
An ce, akalla mutane 43 daga cikin waɗanda suka ci abincin sun samu sauki kuma an sallame su daga asibiti, yayin da wasu 11 ke jinya a halin yanzu.
A halin da ake ciki, akwai wasu mutane 20 da ke cikin mawuyacin hali a sashin kulawa ta musamman a Asibiti sakamakon gubar abincin.
Sakamakon binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa daga gidan abinci guda ne duk wadanda abin ya shafa suka sayi abincin.
Hukumar birnin Riyadh ta kulle gidan abincin da ake zargi, sai dai ba su bata tabbacin yaushe za a bude shi ba.
