Featured
Magidanci dan shekara 71 ya yiwa yar masu haya a gidansa ciki
An kama wani dan shekara 71 bisa zargin yin lalata da ’yar wani magidanci da ke haya a gidansa ’yar shekaru 14, har ta samu juna biyu.
Tsohon wanda ma’aikacin asibiti ne an kama shi yana lalata da yarinyar ’yar shekara 14 a cikin bandaki a Karamar Hukumar Ifo ta Jihar Ogun.
Yarinyar ta shiga bandakin gidan ne domin yin wanka, amma bayan ’yan mintoci sai mai gidan ya bi ta cikin bandakin inda ake zargin ya yi lalata da ita.
Wasu mazauna garin ne suka gan shi, lamarin da ya sa ’yan sanda daga hedikwatar yankin Ajuwon suka kama shi.
Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar.
Omolola ya kuma ce an kai yarinyar Asibitin Tamara da ke Akute, kuma sakamakon gwajin da likitocin suka gudanar ya nuna cewa ba wannan ne karon farko ba, domin kuwa yarinyar na dauke da cikin makonni shida.
