Connect with us

Featured

Nijar Ta Kaddamar Da Rigakafin Sankarau Bayan Cutar Ta Hallaka Mutane 123

 

Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani sabon gangamin yaki da cutar sankarau a sassan kasar sakamakon yawaitar alkaluman mutanen da ke kamuwa da cutar idan aka kwatanta da adadin da kasar ta gani a bara.

Zuwa tsakiyar watan Aprilu Nijar ta sanar da adadin mutane dubu 2012 da suka kamu da cutar ta sankarau ciki har da wasu 123 da cutar ta kashe, lamarin da ya tilasta fara gangamin rigakafin a farkon watan nan kan yaran da shekarunsu ya faro daga 1 zuwa 19.

A bara Nijar ta ga adadin mutane dubu 1 da 389 da suka harbu da cutar sankarau a irin wannan lokaci da jumullar mutum 72 da cutar ta kashe a makwanni 16 na farkon shekarar, alkaluman da suka ninka a bana.

Sashen labarai na African News ya ruwaito yadda iyalai da dama ke ci gaba da dafifi zuwa cibiyoyin rigakafin don yiwa yaransu a wani yanayi da ake fama da matsanancin zafi a sassan kasar ta Sahel.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranakun yau Alhamis da gobe Juma’a, jami’an rigakafin za su bi makarantu don tabbatar da ganin kowanne dalibi ya karbi rigakafin.

Jami’in lafiya Abdou Mamou Siddo ya bayyana cewa aikin rigakafin zai kuma bi gida-gida a ranakun Asabar da Lahadi duk dai a yunkurin dakile yaduwar wannan cuta mai hadari.

Sassan birnin Yamai ke matsayin kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar ta sankarau da kusan kashi 52.2, sai kuma yankunan Agadez da Dosso.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet