Connect with us

Featured

Gwamnatin Kogi Ta Sanar Da Tabbacin Yin Garkuwa Da Daliban Jami’ar CUSTEC

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da sace dalibai tara na jami’ar CUSTEC . da ke Osara Okene.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Usman Ododo ya baiwa al’ummar jihar tabbacin dawowa da daliban da aka sace.

Daliban da ke karatun jarabawar da za su yi, an sace su ne a ranar Alhamis da daddare bayan da ‘yan bindiga suka kai hari jami’ar da misalin karfe 9 na dare.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun shigo cikin daji ne, inda suka shiga dakunan karatu uku sannan suka fara harbin iska don tsorata daliban.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar a ranar Juma’ar nan, ya bayyana cewa, nan take aka samu rahoton, gwamnan “ya tashi jami’an tsaro don bin diddigin masu garkuwa da mutane tare da tabbatar da ceto daliban da aka sace tare da damke wadanda suka yi garkuwa da su. ”

Fanwo ya bayyana cewa yayin da “aka samu rahoton bacewar dalibai tara,” jami’an tsaro da mafarauta na yankin na kokarin ganin an ceto daliban da aka sace.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Gwamnatin jihar ta yabawa kokarin jami’an tsaro da mafarauta na yankin bisa kokarinsu. Hakan ya kasance kamar yadda Ododo ya ba da umarnin a sanya jami’an tsaro a kewayen dukkanin manyan makarantun jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet