Connect with us

Featured

Ana Zargin ‘Yan Ta’adda Sun Kai Kazamin Hari Garin Bilbis A Jihar Zamfara

‘Yan Ta’adda sun kai wani mummunan hari a garin Bilbis da ke Jihar Zamfara inda suka kashe mutane kusan 20 da suka kunshi maza da mata da kuma kananan yara.

Rahotanni sun ce wadannan ‘yan ta’adda sun kai harin ne ranar alhamis inda suka kwashe sama da sa’oi 2 suna aika aika tare da jikkata mutane da dama a garin, kuma yanzu haka wasu daga cikin su na asibiti inda suke karbar magani.

Dan Wasa Mbappe Ya Sanar Da Kawo Karshen Kwantiraginsa Da PSG

Shaidun gani da ido sun bayyanawa Jaridar Premium Times cewar, ‘yan ta’addan sun kai harin ne a kan babura, inda suka toshe duk hanyoyin shiga garin, tare da kai hare hare kan jama’a.

Bayanai sun ce, wasu daga cikin wadanda aka kashe na daga cikin wadanda suka nemi guduwa domin tsira da rayukan su, yayin da wasu kuma har cikin gidajen su aka hallaka su.

Rahotanni sun ce a safiyar ranar Juma’a aka yi janaizar wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan kazamin harin.

‘Yan Najeriya Sama Da Miliyan 30 Za Su Fuskanci Matsananciyar Yunwa — IRC

Garin Bilbis da kuma karamar hukumar Tsafe sun gamu da munanan hare haren ‘yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a jihar Zamfara a yan watannin da suka gabata.

Mutanen yankin sun dade suna gabatar da bukatar girke musu karin jami’an tsaro domin tinkarar wadannan bata gari, amma har yanzu babu cikkaken zaman lafiyar da aka gani a garuruwan dake karamar hukumar.

Garuruwan Tsafe da Zurmi da Maradun da Anka da Bungudu a Jihar Zamfara da makotanta na Katsina da Kaduna da Neja da kuma Sokoto sun zama dandalin zubar da jini daga wadannan ‘yan ta’addan da basa mutunta rayukan jama’a.

Yanzu haka garuruwa da dama a wadannan jihohi sun zama kango saboda yadda mutanen dake cikin su suka fice domin komawa birane idan suke zaton tsira da rayukansu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet