Labarai
Sarkin Tikau Na Jihar Yobe Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
Sarkin Tikau a Yobe, Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn-Grema, ya rasu.
Kanin sarkin, Alhaji Abubakar Talba ne ya tabbatar da rasuwar a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa a Damaturu ranar Asabar.
Talba, wani basaraken masarautar Tikau, ya ce Ibn-Grema ya rasu a Potiskum da misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma’a.
“Eh, zan iya tabbatar muku cewa Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya. Ya haura shekara 70 a lokacin rasuwarsa,” inji shi.
Yariman ya ce marigayin wanda ya kasance shugaban aji na farko, za a yi jana’izarsa da karfe 4 na yammacin ranar Asabar din nan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
NAN ta ruwaito cewa Ibn-Grema, wanda fadarsa take a karamar hukumar Nangere, shine babban sarkin Karekare.
An nada shi a matsayin sarki a ranar 25 ga Yuli, 2001, kuma ya shafe shekaru 23 akan karagar mulki kafin rasuwarsa.
NAN
