Labarai
‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Jami’in Hukumar FIRS A Abuja
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun harbe wani matashi mai suna Khalid Bichi a Maitama, Abuja, a daren Juma’a.
Bichi, wanda aka ce ma’aikaci ne na Hukumar Tara Haraji ta Kasa, an ce maharan sun kashe shi ne daf da karfe 9 na dare a lokacin da ya ke neman abinci, in ji Guardian.
Rahotanni sun ce an harbe shi sau da dama.
Daga nan ne aka garzaya da shi babban asibitin Maitama, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, Bichi ya shahara da yin taka-tsantsan a shafukan sada zumunta da sunan mai amfani da @Khalid Bichi kuma yana da alaka da manyan ‘yan siyasa.
Za a yi jana’izar marigayin a yau da karfe 1:30 na rana bayan sallar jana’izar da aka yi a Abuja National.
