Connect with us

Featured

Wasu ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji 5 Da Wasu Fararen Hula Da Dama A Katsina

Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a wani sansanin soji da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, inda suka kashe sojoji biyar tare da raunata wasu 11 a ranar Lahadi.

Wakilin Jaridar Daily Trust ya tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kuma kashe wasu fararen hula a jiya a kauyen Yarmalamai.

Jaridar Premium Times ta ruwaito wata sanarwa ta cikin gida na sojoji wadda ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na rana a ranar Lahadi.

Takardar ta ce sama da ‘yan ta’adda 200 dauke da manyan makamai karkashin jagorancin wani sarkin ta’addanci, Ado Aleiru, sun kai hari a sansanin sojoji da ke kauyen ‘Yar Malamai.

Haka kuma an kashe wani dan kungiyar ‘yan banga mai suna Aliyu Tukur a harin.

Sanarwar ta ce: “Harin ta’addancin da aka kai a sansanin soji ya yi sanadin jikkata da kuma mutuwar jami’an soji.

“Bayan samun labarin, Supol Faskari, ya zayarci wurin tare da tawagarsa, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar yayin da aka kuma kirayi rundunar hadin gwiwa, aka kuma mayar da martani cikin gaggawa.

“An kwashe sama da sa’o’i biyu ana gwabza kazamin fadan daga rundunar sojojin sama; abin bakin ciki shi ne ne sojoji biyar da wani dan banga daya mai suna Aliyu Tukur mai shekaru 30 sun rasa rayukansu.

“Sojoji 11 sun samu raunuka daban-daban na harbin bindiga, duk wadanda suka jikkata sojoji sun garzaya da su asibiti, an kuma kwashe gawarwakin duka.

“Harin ya kai ga janye sauran sojojin da suka rage daga kauyen zuwa wani sansani da ke kusa da shi mai tazarar kilomita 25 a kauyen Ali Kere saboda yawan hasarar da aka samu.

“’Yan bindigan kuma sun samu raunuka sosai amma sun yi nasarar kawar da su daga wurin. Mazauna yankin a halin yanzu suna ƙaura.

Wata majiya mai tushe a jihar ta shaida wa Jaridar Daily Trust a jiya cewa lamarin ya faru ne tsakanin sojoji da ‘yan ta’addan a kusa da wani sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari.

Ya ce sojojin na rakiyar mazauna kauyen Yarmalamai, “wadanda ba su iya zuwa ko ina ba tare da rakiyar sojoji ba saboda matsalar tsaro.

Ba a samu jin ta bakin babban kwamandan sojojin da ke Abuja ba a daren jiya saboda kiran wayar salular daraktan yada labarai na tsaro, Edward Buba ya nuna cewa “ba za a iya samumsa ba”.

Hakazalika, kakakin rundunar sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, shi ma bai amsa sakon WhatsApp da aka aika masa ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a tsawon shekarun da suka gabata, yankunan da lamarin ya shafa na fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga, kuma an fuskanci matsalar noma da sauran harkokin tattalin arziki.

Sai dai a baya-bayan nan, hadin gwiwar jami’an tsaro tare da hadin gwiwar leken asiri ta sama sun kashe ‘yan ta’adda da dama a sassa daban-daban na jihar Katsina, inda jama’ar yankin ke fatan shiga gonakinsu a wannan damina.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet