Featured
Sabon Tsarin Biyan Kudin Wutar Lantarki Zai Kashe Kananan Masana’antu
Kungiyar masu kananan masana’antu na Najeriya reshen jihar Kano, sunyi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da kudirinta na karin kudin wutar lantarki a kasar don gudun durkusar a bangaren kananan masana’antu.
Shugaban kungiyar Aminu Ibrahim Kurawa ya bayyana damuwar sa kan lamarin lokacin da yake jawabi a taron manema labarai a kano, inda yace haka ya shafesu idan akayi la’akari da adadin abinda suke samarwa a yanzu. Ya bayyana karin kudin wutar lantarkin zai jawo rasa aiki ga mutane da dama sannan hakan barazana ne da zai iya jawo matsalar tsaro a kasa.
“Munyi matukar damuwa game da karin kudin wutar lantarki a Najeriya, wanda hakan ya jefa kananun masana’antu cikin wani hali, duba da irin halin da dama suke fuskanta.
Wannan karin kudi zai kara durkusar da kananun masana’antu kuma hakan barazana ce da zata haifar musamman bangaren tsaro duba da irin halin da ake ciki a kasar.
Bangaren mu yana taimakawa sosai musamman wajen taimakawa tattalin arzikin kasa ya kara habbaka, musamman wajen kirkirar hanyoyin daukar ma’aikata. Amma hakan bazai yiwu ba matukar muna fuskantar irin wadannan tsari na karin kudin wutar lantarki a kasa”.
