Connect with us

Featured

Sojoji Sun Ceto Mutane 386 Bayan Shekaru 10 A Hannun Boko Haram

Sojoji sun ceto fararen hula 386 daga dajin Sambisa ,bayan kimanin shekara goma da sace su da Boko Haram tayi, kuma mafi yawa mata ne da kakanan yara.

Mai rikon mukamin Babban Kwamandan Birget Din Sojin Kasa Na 7, Birgedia AGL Haruna ne ya bayyana haka ranar Lahadi, yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dajin da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno sakamakon nasarar kammala wani aiki na kwanaki 10 da aka yi wa lakabi da “Operation Desert Sanity 111”.

A cewarsa, an kai farmakin ne da nufin kawar da duk wani burbushin Boko Haram da sauran ’yan ta’adda da ke dajin gami da bayar da dama ga masu son mika wuya su yi hakan.

Janar Haruna ya kara da cewa “kokarin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa mun kawar da ragowar ’yan ta’adda a Sambisa, tare da bai wa masu son mika kansu damar yin hakan.

“Da wannan aiki, muna sa ran da yawa daga cikinsu za su mika wuya kamar yadda suka fara.

“Mun kuma ceto wasu fararen hula guda 386 a ranar 17 ga Mayu, 2024; kuma na tabbata adadin zai karu,” inji Haruna.

Janar Haruna ya yaba wa sojojin bisa kwazon da suka nuna, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet