Featured
Kotu ta dakatar da mayar da Sanusi a matsayin Sarkin Kano
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da tube sarakuna biyar da rushe masarautunsu da gwamnatin jihar ta yi ranar Alhamis.
Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya kuma dakatar da gwamnatin Kano da jami’an tsaro amfani da sabuwar dokar masarauntun jihar wadda aka yi wa gyaran fuska, Gwamna Abba Kabir ya sanya wa hannu a ranar.
Umarnin wucin gadin dai ya shafi shugaban ’yan sanda da hukumar tsaro ta DSS da kuma Sibil Difens, har zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar.
Sarkin Dawaki Babba Aminu Babba Danagundi, ne ya shigar da karar neman hana aiwatar da sabuwar dokar masarautun.
Sabuwar dokar ce ta kai ga dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II a kujerar Sarkin Kano tare da kuma tsige Alhaji Aminu Ado Bayero da kujerar.
Hakazalika ta tube sarakunan sabbin masarutun Bichi, Gaya, Rano da Karaye wadanda tsohuwar Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a shekarar 2019.
Kotun ta ba da umarnin cewa ba za a yi amfani da sabuwar dokar masarautun da aka yi wa gyaran fuska ba har sai ta kammala sauraron karar.
Wadanda ake kara sun ha da Gwamnatin Kano, majalisar dokokin jihar da shugabanta, da kuma hukumomin tsaro da sauransu.
