Featured
Malaman Kano Sun Bukaci Tinubu Ya Dauki Matakin Da Ya Dace Don Samun Zaman Lafiya A Jihar
Wasu Malaman Jihar Kano sun fitar da sanarwa inda suka buƙaci Shugaba Tinubu ya ɗauki duk wasu matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Malaman sun bayyana haka ne a wata sanarwa da suka fitar su 18 a ranar Asabar.
Malaman sun jaddada cewa yanayin da ake ciki dangane da batun rikicin masarautu a jihar, idan ba a bi abubuwa a hankali ba, lamarin zai iya zama wani babban rikici.
Malaman sun buƙaci shugaban ƙasar da ya bar Kanawan sun magance matsalarsu ta cikin gida ba tare da an yi amfani da ƙarfi ba.
A cikin makon nan ne Majalisar Dokokin Kano ta yi doka inda ta rushe masarautun jihar biyar waɗanda gwamnatin baya ta samar.
Bayan haka ne gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano a ranar Juma’a.
Sai dai ranar Juma’a da tsakiyar dare ne Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu da ke Kano, daga nan ya zarce Gidan Sarki na Nasarawa, wanda ke da nisan kimanin kilomita ɗaya daga Gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Wannan dalili ne ya sa jama’a suka soma zargin cewa yana so ya koma kan kujerarsa ta sarauta.
