Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Babbar Sallah
Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin 17 ga watan Yuli da Talata 18 ga watan a matsayin ranakun hutun Babbar Sallah na wannan shekerar.
A cikin wata sanarwa, ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya taya al’ummar Musulmai murna bisa bikin na Babbar Sallah.
Yayi kira ga al’ummar Musulmai da su ci gaba da koyi da dabi’un zaman lafiya da tausayi da sadaukar da kai irin na Annabi Ibrahim, sannan ya bukaci a ci gaba da yiwa Kasar nan addu’ar zaman lafiya da ci gaba.
Ministan ya kuma jadadda kudurin Gwamnatin shugaban kasa Tinubu na bada kariya ga dukiyoyi da rayukan ‘yan Najeriya
