Featured
Aminu Ado Bayero Ya Fasa Jagorantar Sallar Idi a Masallacin Kofar Mata
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya fasa yin hawan Sallah da ya tsara zai yi bayan hukumomin tsaro sun dakatar da Hawan.
Aminu Ado ya sanar da hakan ne a sakon Barka da Sallah da aikawa al’ummar jihar Kano daga gidan Sarki na Nasarawa.
“Dole ne mu kaucewa dukkan wani abu da zai yi barazana ga zaman lafiya da rayuka da dukiyoyin al’ammar da muke shugabanta, a kan haka ne muka dakatar da hawan Sallah na al’ada a wannan karan.
” Matakin da muka dauka biyayya ne ga jami’an tsaro da kuma son zaman lafiya”.
Aminu Ado ya kuma taya shugaban kasa da Gwamnan Kano murnar bikin Sallah.
Shima Babban dan majalisar Aminu Ado, Aminu Babba Dan Agundi ya ce Sarkin zai jagoranci Sallar idi ne a gidan Nasarawa da karfe 8 na Safe.
A safiyar yau ne dai wata takarda dake yawo a kafafen sada zumunta ke bayyana cewa tsohon Sarkin zai jagoranci Sallar idi a masallacin Kofar mata inda Sarkin Kano na 16, Malam Muhammad Sanusi na II zai jagoranci Sallar.
