Featured
Sarki Sanusi Ya Jagoranci Hawan Sallah a Kano
Tun da farko Sarkin ya jagoranci Sallar idi da huduba a masallacin Juma’a na Kofar Mata.
An gudanar da Sallar ne a Masallacin Sheikh Tijjani sakamakon ruwan sama da aka kwana ana yi a Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf da jami’an gwamnati ne suka yi Sallah tare da Sarkin.
Jami’an tsaro na ‘yan sanda da Civil Defence sun samar da tsaro a yayin hawan Sallar.
Sarki Sanusi ya zagaya ta Kofar Wambai zuwa gidan Shettima inda ya karbi gaisuwa daga dubban mutane.
Hakan na zuwa ne bayan ‘yan sanda sun sanar da dakatar da Hawan na Sallah.
Sai dai Gwamnatin jihar ta Kano ta ce bada yawunta a ka dakatar ba.
A gefe guda kuma Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya jagoranci Sallah a masallacin gidan Nasarawa.
