Featured
Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi ya yi kira da shugabanni su ɗauki matakan saukakawa al’umma
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na III yayi kira ga dukkan shugabanni a matakai daban-daban da su dau matakan magance matsin tattalin arziki da ake fuskanta.
A jawabin da yayi jim kadan bayan Sallar Idi a filin Idi na Fakon Idi, Sarkin ya ce Najeriya na fuskantar kalubale masu tarin yawa yayin da ‘yan kasa ke fuskantar matsin tattalin arziki.
A cewarsa akwai bukatar kara himma wajen magance wahalhalun da ‘yan Najeriya ke sha.
Sannan ya yi kira kan daukar matakai wajen magance matsalar tsaro a kasar nan.
“Dole ne shugabanni suji tsoron Allah kuma su yi aiki wajen kyautatawa al’umma”, inji shi.
Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su zamo masu son zaman lafiya da kishin kasa.
