Featured
Tsananin Zafi: Saudiyya ta dakatar da Alhazai daga jifan Shedan na tsawon awanni 5
Ma’aikatar lura da aikin Hajji da Umarah ta Saudia ta dakatar da Alhazai daga zuwa Jamarat wajen jifan Shedan daga karfe 11 na safe zuwa 4 na yamma saboda tsananin zafi.
Ministan ma’aikatar, Dakta Abdulfattah Bin Sulaiman ne ya fitar da sanarwa a yau Litinin a Mina dake birnin Makkah.
Ya ce matakin ya zama dole domin tabbatar da lafiyar mahajjata a tsananin zafi da ake fuskanta.
“A don haka, an dakatar da Alhazai daga zuwa Jamarat domin jifan Shedan daga karfe 11 na safe zuwa 4 na yamma”.
Ya ce za a zuba jami’an tsaro a sansanin alhazan domin tabbatar da bin dokar.
