Featured
Tsananin Zafin Rana: Alhaji Dan Najeriya Ya Rasu a Hanyarsa ta Zuwa Jifan Shedan
Wani Alhaji dan Najeriya ya rasu a hanyarsa ta zuwa Jamrate domin jifan shedan saboda tsananin zafi.
Shugaban tawagar likitocin Najeriya, Dakta Abubakar Adamu ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai a garin Mina na kasar Saudia.
Idan za a iya tunawa dai, ma’aikatar Hajji da Umarah ta kasar Saudia ta dakatar da Alhazai daga zuwa Jifan Shedan daga 11 na safe zuwa 4 na yamma saboda tsananin zafi.
Shugaban tawagar Likitocin na Najeriya ya ce sun fadakar da Alhazai kan matakan kaucewa shiga rana da zafi.
Ya shawarci Alhazan da su dinga amfani da Lema domin kariya daga zafin rana.
“Ana shawartar Alhazai da su dinga bin matakan kariya na lafiya da aka samar.
” Alhazai su guji fita da tsakiyar rana kuma su dena tafiya cikin rana”.
Rahotanni sun bayyana cewa sakamakon zafin ranar, Alhazai da dama sun rasa ransu na kasashe daban-daban.
