Connect with us

Featured

Babbar Kotun Tarayya Da Kotun Masana’antu Ba Su Da Hurumin Yanke Hukunci Kan Al’amuran Masarautu- Femi Falana

A yayin da babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a, Justice Liman ke shirin yanke hukunci kan rikicin masarautar Kano, fitaccen lauyan kare hakkin dan’adam mai mukamin SAN, Femi Falana ya bayyana cewa babbar kotun tarayya da kotun masana’antu ta kasa ba su da hurumin yanke hukunci kan al’amuran masarautu.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a jiya Talata, Falana ya soki kotunan biyu kan yadda suka bai wa kansu hurumin sauraren ƙara a kan rikicin, inda ya ce hakan “kuskure ne matuka” da rashin gaskiya a karkashin sashe na 251 da 254 (C) na kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Ya kara da cewa wadannan hukunce-hukuncen sun saɓa wa hukuncin kotun koli da na kotun daukaka kara a kan lamarin.

Falana ya yi nuni da cewa yadda babbar kotun tarayya ta shiga cikin rigingimun da suka shafi tsige sarki Aminu Ado Bayero da kuma dawo da sarki Muhammadu Sanusi ll a matsayin rashin mutunta hukuncin da kotun koli ta yanke kan shari’ar Tukur da gwamnatin jihar Gongola (1987) 4. (117) 517.

A wannan shari’ar, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa ƴancin zama sarki ba wani hakki ne na asali da tsarin mulki ya ba da shi ba, don haka babbar kotun tarayya ba ta da hurumin yin hakan.

Ya bayyana cewa, “Shiga babbar kotun tarayya a kan takaddamar da ta taso daga tsige Sarki Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna da kuma batun dawo da Sarki Sanusi Lamido Sanusi, ya saɓa da hukuncin Kotun Koli a Tukur da Gwamnatin Jihar Gongola ne,”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantpusulabetvdcasinograndpashabetmarsbahisholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetmatadorbetonwinimajbetmatbetholiganbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantsahabetsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet