Featured
Yanzu-Yanzu: APC ta nemi a ayyana dokar ta baci a jihar Rivers
Shugabancin jam’iyyar APC na jihar Rivers, yayi kira da gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta baci a jihar.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar a jihar Rivers, Chief Tonu Okocha ne yayi kiran yayin taron manema labarai a birnin Fatakwal a yau Laraba.
Ya ce “Jihar Rivers na cikin yaki kuma kowa yasan mutumin dake da hannu a wannan lamari.
” Gwamna ya gaza, ‘yan sanda ma haka a don haka APC ke neman a ayyana dokar ta baci a jihar Rivers a matsayin hanyar magance wannan tashin hankali, ina kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar mataki”.
