Featured
Yanzu-Yanzu: Mutane 21 Sun Rasu Sakamakon Kamuwa Da Cutar Amai da Gudawa a Jihar Legas
Mai baiwa gwamnan jihar Legas shawara a fannin lafiya, Dakta Kemi Ogunyemi ta ce adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar amai da gudawa ya karu zuwa 401 inda mutane 21 suka rasu.
Acewarta an fi samun yawan masu kamuwa daga cutar daga Island da Kosofe da Eti Osa.
Bayanin hakan na dauken ne cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya, Tunbusun Ogunbanwo ya fitar.
“Biyo bayan bayanai da ya gabata kan bullar cutar amai da gudawa a jihar Legas, inda aka samu mutanen da suka kamu 350 da rasuwar 15, mai baiwa Gwamna shawara kan fannin lafiya, Dakta Kemi Ogunyemi ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar a yanzu ya kai 401 a fadin jihar Legas”.
