Featured
Kotun tafi da gidanka ta ci tarar ‘yan kasuwar Bachirawa kan rashin tsafta
Kotun tafi da gidanka ta kwamitin tsaftar muhalli a jihar Kano ta ci tarar mayankar dabbobi ta Bachirawa Naira dubu dari 3 bisa gaza tsaftacce mayankar.
Mai shari’a Auwal Yusuf Sulaiman wanda ya bada umarnin ya ce an samu Mahautan da laifin barin wajen sana’ar babu tsafta wanda hakan ka iya yin illa ga lafiyar al’umma.
Haka kuma kotun ta bukaci ‘yan kasuwar mayankar su biya tarar dubu dari 3 kan kin yin biyayya ga dokar tsaftar muhalli ta karshen wata.
A gefe guda kuma kotun taci tarar ‘yan kasuwar Albasa ta Bachirawa Naira dubu dari 2 kan samun kasuwar cikin yanayin tsafta.
Haka kuma kotun ta umarci shugabannin kasuwar su bayyana gaban kwamitin lura da tsaftar na ma’aikatar muhalli ta jihar Kano.
