Featured
EFCC ta kafa kwamitin bincikar Jami’anta da ake zargi da cin zarafin wata mata a Otel
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ta kafa kwamitin ladabtarwa da zai binciki jami’anta guda biyu da ake zargi da cin zarafin wata mata yayin samamen da suka kai a wani Otel a birnin Legas.
Dele Oyewale, mai magana da yawun EFCC wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ya ce jami’an za su gurfana gaban kwamitin a yau Litinin.
Oyewale ya ce shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya kafa kwamitin ladabtarwar domin bincikar jami’an kan zargin cin zarafin matar wacce ma’aikaciya ce a Otel din Regional dake Ojo a Legas.
Wani faifan bidiyo dai ya yadu a shafukan sada zumunta inda aka nuna jami’an EFCC na samame a otel din a ranar Alhamis da ta gabata.
“Olukoyede ya bada umarnin kama jami’an guda 2 kuma ya umarce su su gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.
“An tsara zasu gurfana gaban kwamitin a yau Litinin a ofishin hukumar dake Abuja”.
Acewar sanarwar za a hukunta duk jami’in da aka samu da laifi kan batun.
