Featured
NUC ta amince da karin kwasa-kwasai ga cibiyar karatu daga nesa ta jami’ar ABU
Hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC ta amince da karin darussa ga cibiyar koyo da koyarwa daga nesa ta jami’ar Ahmadu Bello, Zaria daga kakar karatu ta 2023 zuwa 2024.
Karin kwasa kwasan sun hada da: Digiri a fannin aikin Jarida da digiri a fannin kimiyar dakin karatu da digiri na biyu a fannin kula da haddura da annoba.
Hakan yasa cibiyar a yanzu na gudanar da karatu a fannoni 21 inda a baya take koyarwa kan fannoni 6 kadai a shekerar 2020.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Darktan hulda da jama’a na jami’ar, Auwal Mohammed ya fitar.
A wata wasika mai kwanan wata 11 ga Yuni wacce ke dauke da sa hannun mai rikon mukamin Darakta a fannin karatu daga nesa da na kafar Internet, Dakta Funmilayo Morebise, wacce take dauke da amincewar inda aka mikawa shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.
A wasikar da hukumar ta aika ga jami’ar ta bukace cibiyar da ta tabbatar da ingancin kwasa kwasan da za a dinga koyarwa.
