Featured
Kotu ta soke zaben fidda gwani na PDP a Edo
Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja a yau Alhamis ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a jihar Edo.
Asue Ighodalo ne dai ya lashe zaben wanda ya gudana a watannin baya.
Mai shari’a, Inyang Ekwo a hukuncin da ya yanke ya ce zaben fidda gwani da PDP ta yi a ranar 22 ga watan Fabarairu bai bi tanadin dokar zabe ba ta 2022 da kuma ka’idojin fitar da dan takara na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Wakilan masu zabe 381 ne dai dake biyayya da tsohon mataimakin gwamnan jihar da aka tisge, Philip Shaibu suka shigar da karar.
