Connect with us

Featured

Yansanda sun kama wasu ƴan bindiga 5 bayan musayar wuta a Abuja

Yan sanda sun kama ’yan bindiga guda biyar bayan musayar wuta da su a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

An kwato bindigogi kirar AK-47 da wata mata a hannun ’yan bindigar, wadanda aka kama a dajin da ke tsakanin yankin Gwagwa Dei-Dei da ke wajen garin Abuja.

Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ya sanar a safiyar Alhamis 04 07 2024, cewa ’yan bindigar sun shiga hannu ne a samamen kwana uku da rundunar ta gudanar a yankin.

Yace bayan samun bayanai kan ayyukan bata-garin ne ’yan sanda suka yi dirar mikiya a maboyar ’yan bindigar, inda bayan musayar wuta suka kamo su, dalilin garkuwar da aka yi da mutane ranar 12 ga watan Yuni, 2024.

Ana zargin sun karbi kudin fansa Naira miliyan 12, daga iyalan wasu daga cikin mutanen da suka sace, duk da cewa masu garkuwar sun kashe biyu daga cikin mutanen da suka sace.

A cewar Igwe, ’yan bindigar, wadanda duk matasa ne sun amsa laifin da ake zargin su na addabar yankin da sace mutane domin karbar kudin fansa.

CP Igweh, ya ce da zarar rundunarsa ta kammala bincike za ta gurfanar da su a kotu domin su girbi sakamakon abin da suka shuka.

Sannan ya ba wa jama’a tabbacin yin aiki tukuru domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummah.

Daga nan ya ja hankalin mutane da su kasance masu lura tare da kiran wadannan lambobin kar-ta-kwana a duk lokacin da bukatar hakan ya taso: 08032003913, 08028940883, 08061581938, and 07057337653.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet