Featured
Kotu ta dage sauraron karar da El-Rufai ya kai majalisar dokoki ta Kaduna
Babbar kotun tarayya dake zamanta a jihar Kaduna ta dage sauraron karar da tsohon Gwamna Nasiru El-Rufai ya shigar gabanta zuwa 17 ga watan Yuli.
Mai shari’a, RM Aikawa ne ya dage zaman shari’ar domin baiwa wadanda ake kara damar shigar da bayanan bukatunsu.
A watan Yuni ne dai El-Rufai ya shigar da karar majalisar dokokin Kaduna kan ikirarin cewa gwamnatinsa tayi badakalar kudade Biliyan 423.
Tsohon gwamnan ta hanyar lauyansa, Abdulhakeem Mustapha ya shigar da karar ne kan zargin take masa hakki a babbar kotun.
A ranar 5 ga watan Yuni ne majalisar dokokin jihar Kaduna ta bada shawarar binciken El-Rufai kan zargin badakalar kudaden al’umma.
Majalisar ta bada shawarar ne bayan kwamitin wucin gadi da ta kafa ya mika rahotansa na bincikar gwamnatin Nasiru El-Rufai.
A yayin zaman kotun na yau, lauyan majalisar, Sani Katu ya ce wadanda yake wakilta suna kan aikin gabatar da korafinsu kan hurumin kotun game da shari’ar.
Katu ya nemi kotun ta kara musu lokaci don gabatar da bukatunsu.
