Featured
Rivers: Kotu ta dakatar da ‘yan majalisa daga yunkurin tsige Gwamma Fubara
Babbar kotun jihar Rivers dake zamanta a birnin Fatakwal ta bada umarnin wucin gadi ga babban mai shari’a na jihar sakataren majalisar jihar kan kada su yi mu’ammala da shugabancin majalisar karkashin jagorancin Martins Amaewhule.
Umarnin kotun da mai shari’a Jumbo Stephen ya bayar ya kuma dakatar da mutanen biyu daga yin aiki da duk wani abu da majalisar ta amince da shi da takardar neman tsige gwamnan.
Antoni janar na jihar ne ya shigar da karar mai lamba PHC/2177/CS/2024.
Kotun ta kuma umarcin bangarorin biyu da su tsaya a matsayar da ake har sai an saurari karar an kuma yanke hukunci.
Kotun ta kuma dage zamanta zuwa 15 ga watan Yuli.
A yau ne dai ‘yan majalisar 26 dake goyan bayan tsohon Gwamnan jihar, Nyesome Wike suka bai wa Gwamna Fubara wa’adin kwanaki 7 kan ya sake gabatar da kasafin kudin jihar.
