Featured
‘Yan majalisar dake goyan bayan Wike sun bai wa Gwamna Fubara wa’adin kwanaki 7 ya sake gabatar da kasafin kudi
Majalisar dokokin jihar Rivers karkashin jagorancin Martin Amaewhule sun bai wa gwamnan jihar, Siminalayi Fubara wa’adin kwanaki 7 ya sake gabatar da kasafin kudin jihar na 2024.
Umarnin ya biyo bayan zaman farko da ‘yan majalisar wadanda ke goyan bayan Wike suka bayan shafe watanni.
Agefe guda kuma daya tsagin majalisar karkashin jagorancin Victor Oko-Jambo suma sun yi zaman majalisar.
Tun da farko dai Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin kudin ga ‘yan majalisar dake goyan bayan shi a lokacin da shugaban ma’aikatansa, Edison Ehie ke jagorantar majalisar.
Ehie da sauran ‘yan majalisar na tsagin Fubara sun amince da kasafin inda gwamnan ya sanya hannu a kai.
