Featured
Zargin Badakalar Kudade: Ganduje zai gurfana gaban babbar kotun jihar Kano
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Ganduje da wasu mutane 6 za su gurfana gaban babbar kotun jihar Kano a ranar Alhamis domin amsa laifukan da suka shafi badakalar kudade da karbar na goro.
Gwamnatin jihar Kano ta jam’iyyar NNPP ce dai ta shigar da karar tsohon Gwamnan gaban mai shari’a, Amina Adamu Aliyu.
A ranar 5 ga watan Yuni ne kotun ta amince da bukatar masu kara na aika sammaci ga wadanda ake kara ta hanyar wallafawa a jaridun Daily Trust da The Nation.
Wadanda ake karar dai su ne: Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsa Ganduje da Abubakar Bawuro da Umar Abdullahi Umar da Jibirillah Muhammad da kamfanin Lamash.
Mai shari’a, Amina Adamu Aliyu ta sanya 11 ga watan Yuli a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraran karar.
