Featured
Shugabar karamar hukumar Wudil ta dauki nauyin karatun mata 30 a fannin kiwon lafiya
Shugabar riko ta karamar hukumar Wudil, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta sanar da bada tallafin karatu ga dalibai mata dake karatu a fannin kimiyya ‘yan asalin karamar hukumar.
Tallafin karatun zai shafi dalibai mata 30 na karamar hukumar inda zai basu damar karatun ilimin jinya a makarantun koyar da ilimin jinya da unguwar zoma dake Gezawa da Madobi da Dambatta.
Da take jawabi yayin bikin bada tallafin, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta yi bayani kan alfanun tallafin karatun da kuma tasirinsa wajen ci gaban ilimi a karamar hukumar.
Ta ce a karkashin shugabancinta, karamar hukumar ta dauki nauyin karatu sama da dalibai dubu 2 a jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote.
Acewarta an bada tallafin ne bisa lura da cancanta sannan wadana suka amfana sun fito daga mazabun karamar hukumar.
Sannan ta yi alkawarin cewa da zarar sun kammala karatunsu za a tura su mazabunsu domin kula da al’ummarsu.
