Connect with us

Featured

Stallion Times ta shirya taron tattaunawa kan samar da shugabanci na gari

Jaridar Stallion Times Media Services, da hadin gwiwar MacArthur Foundation, Sun shirya wata Tattaunawa ta Musamman akan yadda za’a samu Kyakkyawan Shugabanci.

Taron wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 11 ga watan yulin 2024, a Ofishin Kungiyar ‘Yan Jaridu ta ƙasa reshen jihar Kano.

A zaman Tattaunawar Kungiyoyi da dama ne suka halarta, wadanda suka hada da Shugabancin Kungiyar Open Government Partnership, na Jihar Kano da wakilai daga gwamnatin Jihar Kano da Kungiyar ‘yan Kasuwa da Kungiyar Mata da kuma wakilai daga Kungiyoyi masu zaman kansu.

A jawabinsa, Shugaban taron Isiyaku Ahmed, ya bayyana cewa an hada mutane iri daban daban masu ra’ayoyi mabanbanta don a samu hanyar da za a bi wadda za ta samar da alaka mai kyau tsakanin Gwamnati da al’umar gari.

Da yake bayyana hanyoyin da za a bi wajen samun shugabanci mai inganci, Leslie Babangida, yace yana da kyau shugaba ya samu goyon baya da yardar al’umma, ta yadda hakan zai sa ko wajen kamfen ba zai kashe kudi da yawa ba, sannan dole Shugaba ya samu hanyar da zai ringa jin ra’ayin al’umma lokaci zuwa lokaci.

Shima wakilin gwamnati, kuma Director Service Charter Aminu Imam Wali, Yace an kirkiri Ma’aikatar Servicom don a tabbatar yan kasa suna samun jagoranci nagari, Sannan Hukumar ta karbi korafi akan ma’aikaci ko ma’aikatar da ta Gaza sauke nauyin da yake kanta, amma abin takaici sai a dauki lokaci me tsawo babu wanda ya kai wani korafi, duk da ba a samun abinda akeso.

A karshe an cimma matsaya kan cewa duk shekara za a dinga gayyato gwamna ya yi wa al’umma bayanin alƙawuran sa yayi musu a lokacin kamfen, shin ya cika su ko kuwa bai cika ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet