Featured
An jibge karin jami’an tsaro a gidan Sarki a yayin da ake raɗe raɗin yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa
An jibge jami’an tsaro a kofar gidan Sarki dake Kofar Kudu a jihar Kano a yayin da ake rade radin cewa matasa za su fito zanga-zanga kan tsadar rayuwa.
An ta yada batun zanga zangar dai a shafukan sada zumunta inda wasu ke cewa za a gudanar da ita a yau Asabar yayin da wasu ke shirya gudanar da zanga zangar a ranar 29 ga watan Yuli da muke ciki.
Waklinmu da ya ziyarci titin gidan Sarki ya ga an jibge karin jami’an tsaro wanda suka yi shirin ko ta kwana.
An hangi babbar motar jami’an tsaron ‘yan sanda a kofar shiga fadar Sarkin yayin da aka hangi motocin ‘yan sanda da na Civil Defence a titin na gidan Sarki.
Sai dai al’ummar gari na ci gaba da harkokinsu inda ba a hangi tawagar masu ikirarin fitowa zanga zangar ba.
