Featured
Kotu ta dawo da mataimakin Gwamnan jihar Edo da aka tsige
Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja a yau Laraba ta soke tsigewar da majalisar dokokin jihar Edo ta yi Phillip Shuaibu a matsayin mataimakin gwamnan jihar.
Mai shari’a, James Omotosho a hukuncin da ya yanke ya bada umarnin mayar da shi a matsayin mataimakin gwamnan inda ya ce majalisar bata bi ka’idar doka ba wajen tsige shi.
Alkalin ya kuma umarni babban Sufeto janar na ‘yan sanda ya baiwa Shuaibu jami’an tsaron da ake bukata wajen komawarsa ofis don kammala wa’adinsa.
Justice Omotsoho ya kuma soke nadin da aka yiwa sabon mataimakin gwamnan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa Shaibu wanda ke kotun yayin yanke hukuncin ya fashe da kukan dadi bayan sanarwar alkalin.
