Featured
Yahya Bello ya gaza gurfana gaban kotu a karo na 6
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya gaza bayyana gaban babbar kotun tarayya dake Abuja a yau Laraba a shari’ar da ake yi masa na zargin karkatar da kudade sama da Biliyan 82.
An tsara Yahaya Bello zai gurfana gaban mai shari’a Justice Emeka Nwite da safiyar yau Laraba sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu alamar zuwansa kotun.
Kodayake, lauyoyinsa guda 2, Mohammed Aliyu da Adeola Adedipe sun halarci kotun a bisa umarnin da kotun ta bayar.
Ana sa rai Lauyoyin zasu amsa tambaya bayan rantsuwar da suka yi kan cewa zasu gabatar da Yahya Bello a zaman kotun.
Yahaya Bello dai ya kauracewa zaman kotun har sau 6 inda ya nemi a mayar da karar zuwa jihar Kogi.
