Featured
Gwamnatin Legas ta sha alwashin hukunta jami’an bogi dake cin zarafin masu ababen hawa a jihar
Gwamnatin jihar Legas ta sha alwashin kama jami’an bogi da ake zargi da tilasta bin dokokin hanya a wasu yankunan jihar.
Gwamnatin jihar ta bayyana hakane bayan yawaitar samun rahotan jami’an bogi dake ikirarin su jami’an hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa na jihar ne suna cin zarafin ababen hawa.
Ana zargin jami’an na bogi na yin ayyuka a wasu manyan titunan jihar.
Babban sakatare a ma’aikatar sufuri ta jihar, Misra Olawale Musa yayin da yake karin bayani kan lamarin ya ce duk da aikin kawar da mutanen, jami’an na bogi sun ci gaba da ayyukansu na bogi a manyan tituna.
