Featured
Babu mu a zanga-zanga – kungiyar Fulani ta Miyetti Allah
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, ta ce mambobinta ba za su shiga zanga zangar da aka tsara yi kan tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Agusta mai kama wa ba.
Shugaban kungiyar, Abdullahi Bello-Badejo ne ya fadi hakan yayin ganawa da manema labarai a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.
Bello Badejo ya ce, kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ba za ta goyi bayan zanga zangar ba da za a yi a wata mai kamawa.
Sai dai ya ce sun fi aminta da hanyar tattaunawa da mahukunta wajen kawowa ‘yan kasa saukin rayuwa.
Kungiyar ta kuma yaba da kafa sabuwar ma’aikatar kula da kiwo da shugaban kasa Tinubu yayi.
Kungiyar ta nemi masu shirin shiga zanga zangar da su sake tunani domin zanga zangar ka iya haifar da rashin zaman lafiya.
