Connect with us

Featured

Dangote ya buƙaci NNPCL ya sayi matatar man sa

Alhaji Aliko Dangote ya bukaci Kamfanin Mai Na Kasa na Najeriya (NNPCL) da ya zo saye matatar man sa, wadda ita ce ta biyu mafi girma a duniya.

Dangote ya yi wannan furuci na neman NNPCL ta mallake matatar tasa ne cikin takaici, kan dambarwar da ta kunno kai a kan matatar a tsakaninsa da hukumomin kula da bangaren mai na Najeriya.

Wannan dambarwa dai ta hana matatar samun adadin danyen man da take buƙata domin fara samar da tataccen man fetur a kasuwa.

A makon jiya ne Dangote ya yi zargin cewa wasu miyagu a cikin Najeriya da kasashen waje sun sha yin kokarin ganin cewa matatar tasa ba ta fara aiki ba.

Amma daga bisani Hukumar Kula da Albarkatun Mai (MNDPRA) ta bullo tana zargin matatar Dangote da samar da man dizel mara ingancin da ake bukata idan aka kwatanta da wanda ake shigo da shi daga kasashen waje.

Babban Jami’in MNDPRA, Farouk Ahmed, ya shaida wa ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa cewa, a sakamakon haka, Najeriya ba za ta dogara da matatar Dangote domin samar da man da ake bukata a kasar ba.

Farouk Ahmed ya kara da cewa, hasali ma matatar ta Dangote ba ta da lasisin fara aiki a Najeriya.

Ya kuma ƙaryata zargin da ake wa hukumar MNDPRA na neman hana wa matatar Dangote ruwa gudu, ta hanyar rashin samun danyen mai daga kamfanonin hakar mai na kasashen waje.

Sai dai a wata hira ta musamman da ya yi da kafar labarai ta Premium Times, Alhaji Aliko Dangote ya ce, idan NNPCL na so, za su iya zuwa “su saye matatar daga hannuna su gudanar da ita yadda suke ganin ya fi dacewa.

“Sun ce na yi kane-kane na tare komai, alhali ba haka ba ne. Amma babu komai.

“Idan suka saye matatar daga gareni, shi ke nan sun kawo karshen wanda suke ganin ya yi musu kaka-gida,” in ji dan kasuwar.

Tasirin Matatar Dangote

A shekarar 2023 aka kaddamar da matatar Dangote mai karfin tace gangar danyen 650,000 a kullum, wadda aka gina a kan Dala biliyan 19.

Ana kuma kyautata zaton matatar za ta taimaka wajen rage matsalar mai da kuma dogaro da kasashen waje a bangaren.

Hakan zai rage asarar kashi 30% na kudaden da kasar take asara a bangaren musayar kudaden ketare domin shigo da kayayyaki.

A hiharsa da Premium Times, Aliko Dangote ya ce: “Tun shekarun 1970 ake fama da matsalar mai a kasar nan.

“Wannan matata za ta taimaka wajen magance matsalar, amma akwai mutanen da ba su so, saboda tawa ce.

“Sabosa haka a shirye nake in bar musu matatar, NNPCL ta zo ta saya akwai ta ci gaba da gudanar da ita.”

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet