Featured
Tinubu ya mika kudurin dokar mafi karancin albashi ga majalisa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da kudurin dokar mafi karancin albashi ga majalisar dokoki ta tarayya domin sahalewa ya zama doka.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, shugaban kasar da kungiyar kwadago suka amince da Naira dubu 70 a matsayin mafi karancin albashi.
An cimma matsayar ne bayan jerin tattaunawa da dama tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadagon.
Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero ya ce sun amince da Naira dubu 70 tare da kin amincewa da bukatar shugaban kasar na bai wa ma’aikata mafi karancin albashi na Naira dubu 250 amma da sharadin karin kudin mai.
Sannan ya ce za a dinga bibiyar mafi karancin albashin duk bayan shekaru 3 sabanin shekaru 5 a baya.
