Featured
Yanzu-Yanzu: MTN sun sanar da rufe ofisoshin su a Najeriya
Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da rufe dukkan ofisoshinsa dake Najeriya daga yau Talata 30 ga watan Yuli.
Wani jami’i a kamfanin ne ya tabbatar da hakan ga jaridar TheCable.
Majiyar ta ce an dau matakin ne sakamakon farmakin da fusatattun mutanen da aka rufewa layuka suka kai wa kamfanin.
A ranar 27 ga watan Yuli ne dai yan Najeriya da dama suka kai kokensu bayan hana su amsa kira da yin kira a layukan nasu sakamakon rashin tantance lambar NIN dinsu.
A ranar Litinin ne wasu fusatattu masu amfani da layukan suka farmaki ofishin MTN dake Festac a jihar Legas.
