Featured
Jami’an mu na NNPC ba barayi ba ne – Mele Kyari
Shugaban Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya yi watsi da zargin cewa ma’aikatan kamfanin na da hannu wajen shigo da man fetur marasa inganci a ƙasar.
Ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Laraba 07 ga Agusta, 2024.lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar dattawa kan zargin zagon ƙasa a harkar man fetur.
Kyari ya ce a matsayinsa na babban jami’in kamfanin NNPCL, ya fuskanci ƙalubalen da bai dace ba daga kafafen yaɗa labarai da kuma mutanen da ke zargin cewa kamfanin yana aikata abin da zai haifar wa tattalin arzikin ƙasar zagon ƙasa.
“Kamfanin mai NNPCL bai amince ba kuma ba zai yi wa ƙasa ƙarya ba.
“Mu ba masu laifi ba ne kuma ba ɓarayi ba ne. Za mu kare mutuncinmu domin mu yi wa ƙasar nan hidima,” in ji shi.
Da yake yin ƙarin haske, ya bayyana cewa masana’antar mai da iskar gas na cikin wani yanayi, yana mai cewa akwai abubuwan da suka sani amma ba za su iya magana a fili ba har sai lokacin ya zo.
Wannan dai ya biyo bayan cece-kucen da aka samu a bayan nan dangane da kamfanin da kuma yanayin ayyukansa.
